Bisa labarin da aka bayar, an ce, yawan daliban da za su kammala karatun jami'a a yankin Tibet a shekarar 2013 ya kai fiye da dubu 14. A bana, ana gudanar da ayyukan samar da aikin yi ga daliban, da yin kokarin cimma buri a wannan fanni.
Ban da wannan kuma, hukumomin kula da albarkatun kwadago da bada tabbaci ga jama'a na yankin sun gudanar da tarurukan samar da aikin yi don kara samar da dama ga daliban yankin, da kuma tabbatar da shigar da su wajen samun aiki yadda ya kamata. (Zainab)