in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta gabatar da takardar bayani kan ci gaban yankin Tibet
2013-10-22 10:37:01 cri
A yau Talata 22 ga wata, ofishin yada labaru na majalisar gudanarwa na kasar Sin ya gabatar da takardar bayani kan ci gaban yankin Tibet, inda ya yi cikakken bayani kan ci gaban da yankin Tibet ya samu a cikin shekaru 60 da suka gabata.

Tadardar ta yi bayyani cewa, Tibet wani kashi ne na kasar Sin tun lokacin fil azal. A yanzu dai, Tibet ya samu bunkasuwar tattalin arziki, ci gaban siyasa, wadatar al'adu, jituwar al'umma da muhalli mai kyau, kuma jama'arsa suna jin dadin zamansu. Hakan ya bayyana alaman Tibet dake nuna haduwar al'adun da da na zamani a wannan yanki.

Ban da haka, takardar ta nuna cewa, ci gaban da Tibet ya samun ya shaida cewa, kamar yadda jama'ar sauran kasashe suke, jama'ar Tibet ma na da 'yancin amfani da ci gaba na zamani, kuma suna da 'yancin daga matsayin zaman rayuwarsu, tare da zabar hanyar da suke son ta fuskar zaman rayuwa. Don haka ya yi baynin cewa, ci gaban da Tibet ya samu ya dace da yanayin bunkasuwar Bil Adam, hakan kumaya dace da burin jama'ar Tibet, wanda kuma ya kasance sakamakon ci gaban kasar Sin baki daya. (Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China