in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi girgizar kasa ta digiri 6.1 a yankin Changdu na jihar Tibet
2013-08-12 15:57:29 cri
Cibiyar ba da labarai kan aukuwar bala'un girgizar kasa ta kasar Sin ta tabbatar da cewa, a sanyin safiyar yau Litinin 12 ga wata da misalin karfe 5 da minti 23, an samu aukuwar girgizar kasa da karfinta ya kai digiri 6.1 bisa ma'aunin Richter a yankin iyaka a tsakanin gundumomin Zuogong da Mangkang da ke yankin Changdu na jihar Tibet, zurfinsa ya kai kilomita 10 a karkashin kasa, kumar yadda ofishin yanki na lura da abkuwar bala'in ta garin Renguo da ke bakin iyakar gundummomin biyu ta bayyana. Ya zuwa yanzu dai ba a samu ko wane labari kan mutuwa ko raunukar mutane ba.

Bayan faruwar bala'in, gwamnatin jihar Tibet ta kaddamar da aikin ceto cikin gaggawa. Sannan Gwamnatin yankin Changdu kuma ta aiwatar da shirin tinkarar abin da ya faru kwatsam na matsayi na uku, bisa jagorancin Xu Chengcang, shugaban yankin Changdu, 'yan sanda masu kashe gobara, jami'an hukumomin kula da harkokin jama'a da girgizar kasa sun nufi wurin da bala'in ya faru ba tare da bata lokaci ba.

An bada labarin cewa, akwai kauyuka 12 da ke kunshe da mazauna 3476 a garin Renguo, wanda ke da nisan kilomita 51 da gundumar Zuogong, da nisan kilomita 75 da gundumar Mangkang.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China