Hare-haren Boko Haram sun tilastawa 'yan Najeriya 13000 tserewa zuwa Kamaru in ji UNHCR
Miliyoyin 'yan Najeriya sun fice baya bayan nan zuwa kasar Kamaru domin gujewa hare haren mayakan kungiyar Boko Haram daga arewa maso gabashin kasarsu, in ji babbar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD (UNHCR) a ranar Talata. A cewar hukumomin kasar Kamaru, kusan 'yan gudun hijirar Najeriya 13000 suka isa a jihar Adamawa bayan da wasu mayaka suka kai hari tare da kwace garin Mubi a karshen watan Oktoba. 'Yan gudun hijirar sun tsere zuwa biranen Guider da Gashiga dake yankin arewacin Kamaru da kuma Bourha, Mogode da Boukoula dake yankin Grand Nord, in ji hukumar a cikin wata sanarwa a birnin Geneva. A cewar hukumar ta MDD, hukumomin yankunan na Kamaru sun bayyana cewa adadi mafi yawa na wadannan 'yan Najeriya 13000 ya koma Najeriya, tare da zango na karshe Yola, hedkwatar jihar Adamawa, mai tazarar kilomita kimanin 200 daga kudancin Mubi. Hukumomin na Kamaru sun bayyana cewa sun samar da jami'an tsaro masu rakiya domin tabbatar da tsaro ga wadanda suka ratsawa ta kasar Kamaru.
A Yola, hukumar UNHCR ta yi hira da wasu mutanen da suka ratsa ta kasar Kamaru kafin su shigo Najeriya. Yawancin mutane daga cikinsu mata ne da yara kanana. Sun shaidawa ma'aikatanmu cewa iyalai da dama an tilasta musu gudu da kafa, tare da daukar kayayyakinsu kalilan, kana sun yi tafiya bisa tsawon kilomita gomai kafin su samu tsaro a kasar Kamaru in ji sanarwa hukumar. (Maman Ada)