Wani mazaunin yankin da ya ganewa idonsu mai suna Isika Wanzam ya ce, mayakan sun shiga garin ne da safiyar ranar Alhamis ciki a kalla motocin Hilux 30 dauke da gurneti da manyan makamai inda suke kai hari kan gine-gine gwamnati.
Ya ce, mayakan sun kwashe kusan sa'o'i 2 suna ta barna kafin jami'an tsaro su iso, karar abubuwan fashewa da harbin bindiga sun tilasta wa mutane zama a cikin gidajensu. (Ibrahim Yaya)