in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ya bukaci Boko Haram da ta kwance damara
2015-01-20 16:34:28 cri
Jiya Litinin 19 ga wata, kwamitin sulhu na MDD ya zartas da wata sanarwar, inda ya bukaci kungiyar masu tsattauran ra'ayi ta Boko Haram da ta dakatar da aikace-aikacenta na keta hakkin dan Adam da na sabawa dokar jin kai ta kasa da kasa, sa'an nan ta kwance damarar mayakanta.

Bugu da kari, kwamitin sulhu na MDD ya yi allah wadai da hare-haren da kungiyar Boko Haram ta kai a kwanan baya, musamman ma kan yadda ta yi amfani da kananan yara domin kai harin kunar-bakin-wake a birnin Maiduguri na jihar Borno a ran 10 ga wata. Haka kuma kwamitin ya yi kira ga Boko Haram da ta saki dukkanin mutanen da ta yi garkuwa da su ba tare da bata lokaci ba, ciki hada da dalibai 'yan mata 276 da ta sace a watan Afrilun shekarar 2014. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China