in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fiye da 'yan Najeriya 3000 aka tilastawa gudu zuwa Nijar bayan wani harin kungiyar Boko Haram in ji UNHCR
2014-11-29 16:24:42 cri
Hukumar 'yan gudun hijira ta MDD (UNHCR) ta rawaito a ranar Jumma'a cewa wani harin kungiyar Boko Haram a wannan satin kan birnin Damassak dake Najeriya yayi sanadiyyar mutuwar mutane 50 tare da tilastawa mutane a kalla 3000 gudu zuwa jihar Diffa ta kasar Nijar dake makwabtaka da Nijeriya. "Ina zaton Boko Haram ta karbe ikon wurin a ranar 24 ga watan Satumba" in ji kakakin UNHCR dake wurin, 'yan Najeriya na jiran jiragen ruwa domin ratsa ruwan kogin Komadougou Yobe dake raba kasashen biyu. Ta wani bangare, wasu mutanen na kokarin ratsa ruwa ta iyo domin tsirar da rayukansu. Mazauna yankin sun bayyana cewa sun ga mutanen da suka mutu cikin ruwa a lokacin da suka kokarin ratsa ruwan ta iyo. Wasun kuma 'yan Boko Haram sun kashe a lokacin dake kokarin cimma gabobin kogin. A cewar sabbin mutanen da suka iso, masu yawan da suka kaura yawancinsu mata, yara kanana da tsoffi, daga cikinsu wasu sun yi rauni na cigaba da jira daga bangaren bakin kogin Najeriya domin samun isa Nijar. Haka kuma sabbin mutanen da suka iso sun bayyana cewa an kashe fararen hula da dama a yayin harin Damassak, musammun ma matasa. Mayakan kuma sun yi harbi kan mata da yara. Wasu mazauna wurin dai sun yi tunanin cewa harin wata ramuwar gayya ce kan shigar da matasa cikin kungiyoyin sa kai na tsaro da suka samu horo domin su yaki mayakan Boko Haram.

Rikicin Najeriya ya tilastawa mutane fiye da 39,000 gudu zuwa Kamaru a cikin watanni biyu na baya bayan nan ayayin da wasu 2800 suka isa Chadi. A Najeriya, kusan mutane 700,000 suka kaura daga mahallinsu zuwa wasu yankunan kasar a cikin jihohin Borno, Yobe da Adamawa a cewar wasu alkaluman gwamnatin Najeriya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China