Jami'in ya kuma kara da cewa, dukkanin fasinjojin da maharan suka hallaka a farmakin na ranar Alhamis maza. Kaza lika mayakan su sace bas din da mutanen ke ciki bayan sun hallaka su.
Wannan ne dai karo na biyu, da aka samu aukuwar irin wannan ta'asa a yankin na arewa mai nisa a cikin mako guda.
A Talatar da ta gabata ma dai sai da wasu dakarun da ake zaton mambobin kungiyar ta Boko Haram ne, suka kashe wasu direbobin manyan motocin daukan kaya a garin Mora, dake yankin arewa mai nisa na kasar ta Kamaru. (Maryam)