in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An samu fashewar bam a wata tashar motoci a Nijeriya
2014-11-28 16:09:57 cri
Jiya Alhamis 27 ga wata, wata bam ta fashe a wata tashar motoci dake arewa maso gabashin kasar Nijeriya, inda a kalla mutane 35 suka rasa rayukansu, wadanda suka hada da sojoji guda biyar.

Lamarin ya faru a wani wurin dake da nisan kilomita 30 da yammacin garin Mubi dake jihar Adamawa a arewancin kasar Nijeriya. Wadanda lamarin ya faru gaban idanunsu, sun ce, bayan da suka ji karar fashewa, kasa ta girgiza a ko ina, kuma fashewar bam din ta haddasa lalata motoci da dama, an kuma gano gawawaki da dama a wurin.

Ya zuwa yanzu, hukumomin kasar ba su b ada wani karin haske ba kan wannan lamarin da ya faru a ran 27 ga wata ba, kuma babu wata kungiya ko wani mutum da ya dauki alhakin kai harin ba. Amma wasu kafofin watsa labarai na ganin cewa akwai hannun kungiyar Boko Haram kan irin wannan harin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China