Faifan bidiyon ya nuna madugun kungiyar ta Boko Haram na cewa, kungiyar Boko Haram ba ta taba hawa teburin shawara da gwamnatin Nijeriya ba, kuma ba su san wani wakilin su da ake cewa an tattauna da shi ba.
Ya ce, "ba mu cimma matsaya da kowane mutum ba, kama daga kasar Chadi, ko Kamaru, ko Nijeriya. Duk wata magana kan batun kulla yarjejeniyar tsagaita bude wuta karya ce kawai.
Shekau ya kara da cewa ba su da niyyar yin shawarwari da kowane mutum. Kana ya bayyana cewa dukkanin 'yan mata 219, da kungiyar ta yi garkuwasace da su daga jihar Borno sun riga sun rungumi addinin Musulunci, kuma dukkansu sun yi aure.
Kawo yanzu dai ba a san hakikanin lokaci, ko wurin da aka dauki wannan faifan bidiyo ko makasudin fidda shi ba. Sai dai wasu iyalan yaran da kungiyar ta sace, sun bayyana wa kafofin yada labarai cewa, batun shiga addinin Musulunci, ko auren da ake cewa an yiwa 'ya'yan su b a shi ne a gaban su ba. Sun ce abin da yafi damun su shi ne halin da tsaro lafiyar yaran.
Ya zuwa yanzu dai gwamnatin Nijeriyar ba ta ce komai game da wannan faifan bidiyo ba.(Fatima)