Shugabannin da suka halarci taron bisa goron gayyatar shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou, sun hada da shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya, Idriss Deby na Chadi, Thomas Yayi Boni na Benin sai kuma wani minista a fadar shugaban kasar Kamaru da ya wakilci shugaba Paul Biya.
Haduwar shugabannin kasashen ta biyo bayan wani zaman taron ministocin tsaron kasashen CBLT a ranar Litinin, domin tsai da shawarwarin da za su taimaka wajen fita daga wannan matsala da za'a gabatarwa shugabannin a yayin taronsu.
Mahamadou Issoufou, shugaban kungiyar CBLT a wannan karon, ya janyo hankalin gamayyar kasa da kasa a yayin babban taron MDD na baya bayan nan, cewa wani karin kokari da yin hadin gwiwa sun zama dole a bangaren shiyya shiyya da ma kasa da kasa domin samun zarafin fuskantar barazanar kungiyar Boko Haram yadda ya kamata.
Kasar Nijar dai na raba kan iyaka tare da Najeriya bisa tsawon kilomita dubu daya da dari biyar, kuma yawancin al'ummomin kasashen biyu na magana da harsuna kusan daya wato Hausa, Fulatanci da Kanuri. (Maman Ada)