Shugaban ya bayyana haka ne a jiya Laraba yayin a jawabin da ya yiwa 'yan kasar a bikin cikar kasar shekaru 54 da samun 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka inda ya ce, gwamnatinsa ta himmatu wajen kare rayuka da dukiyoyin al'ummarta har ma da 'yan kasashen wajen da ke kasar, sannan ya bukaci kungiyoyin 'yan ta'adda da su hanzarta mika makamansu.
Ya ce, gwamnati ta bullo da wani shiri da nufin sake farfado da tattalin arziki a shiyyar arewa maso gabashin kasar da ke fama da wannan rikici. shirin da shugaban ya ce, ana ci gaba da aiwatar wa a sassa daban-daban na kasar duk da matsalar 'yan ta'addan da ake fuskanta.
Don haka, ya yi kira ga 'yan Najeriya da al'ummomin kasa da kasa da su goyi bayan kokarin da gwamnati da sojojin kasar ke yi na kawo karshen ayyukan ta'addanci a Najeriya.(Ibrahim)