Kakakin cibiyar tattara bayanai ta kasar Najeriya Mike Omeri wanda ya bayyana hakan a Abuja ya ce, gwamnati za ta bullo da wasu dabaru don tabbatar da cewa, mayakan da suka mika wuya sun samu wani horo da zai wanke musu tunanin tsattsauran ra'ayi a zukatansu yayin da wadanda suka ki mika makamansu kuma za su fuskanci hukuma.
Omeri ya kuma shaidawa manema labarai a Abuja cewa, kisan shugaban kungiyar ta Boko Haram Abubakar Shekau da dakarun kasar suka yi, wani mummuna koma baya ne ga magoya bayansa, lamarin da ya tilasta wa 'yan ta'adda da dama guduwa, kana ya karfafa wa dakarun kasar kwarin gwiwa a yakin da suke da mayakan na Boko Haram.
Masu sharhi na cewa, wannan ci gaba ya kara tabbatar da cewa an kusa kawo karshen gwagwarmayar tsawon shekaru da Najetiya ke yi da mayakan Boko Haram, kungiyar da ta haifar da babbar baraza a yammacin Afirka.
A ranar Lahadi ne hedkwatar tsaron kasar ta tabbatar da cewa, wasu mayakan Boko Haram sun fara mika wuya, inda wasu 148 suka mika makamansu. (Ibrahim)