Yarjejeniyar ta shafi kuma sako dalibai 'yan mata fiye da 200 da aka sace a cikin watan Afrilun da ya gabata. An cimma wannan yarjejeniya tsakanin babban sakataren musammun na shugaba Goodluck Jonathan, Hassan Tukur da kuma wakilin kungiyar Boko Haram, Danladi Ahmadu, a cewar kakakin cibiyar watsa labarun kasa, Mike Omeri.
Mista Badeh ya tabbatar da cewa ya baiwa rundunar sojojin kasar umurni da su girmama wannnan yarjejeniyar tsagaita bude wuta.
A nata bangare, kungiyar Boko Haram ta ba da tabbacin cewa dukkan dalibai 'yan mata da sauran wasu mutanen da aka sace suna nan cikin koshin lafiya. (Maman Ada)