Yau Alhamis 9 ga wata da safe, shugaba Uhuru Kenyatta na kasar Kenya ya koma birnin Nairobi, hedkwatar kasar bayan da ya kammala halartar zaman kotun hukunta manyan laifuffuka ta kasa da kasa ICC da ke Hague.
Ranar 8 ga wata Laraba ne, Kenyatta ya halarci zaman da kotun hukunta manyan laifuffuka ta kasa da kasa ta shirya dangane da tukumar da take masa. Don haka ne ma ya zama shugaba na farko a duniya da ke kan mulki ya halarci zaman kotun ta ICC. Duk da cewa, ya musunta tuhumar da ake masa.
Kafin ya tashi daga Kenya a ranar 7 ga wata, ya sanar da mika ragamar shugabancin kasar ga mataimakinsa William Ruto don ya gudanar da ayyukan shugaban Kenya na wucin gadi.
Bayan da Kenyatta ya koma gida, za a maido masa da matsayinsa na shugaban Kenya.
Bayan wannan zama, kotun hukunta manyan laifuffuka ta kasa da kasa za ta yanke shawara kan ko za ta ci gaba da gudanar da shari'a kan Kenyatta ko kuma za ta sa aya ga lamarin. (Tasallah)