in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Kenya zai halarci taron CPI
2014-10-07 16:28:23 cri
Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya bayyana a ranar Litinin cewa zai halarci a ranar Laraba a wani "taron daidaita kome" na kotun hukunta manyan laifuffuka ta kasa da kasa CPI a matsayinsa na dan adam ba a matsayinsa na shugaban kasa ba, taron da zai taimaka wajen shirye-shiye shari'arsa.

Da yake jawabi a gaban mambobin majalisar dattawan kasar da na 'yan majalisa, mista Kenyatta ya sanar da nada mataimakin shugaban kasar, William Ruto, a matsayin mai maye gurbin a fadar shugaban kasar har sai ya dawo daga birnin Haye. Mista Kenyatta ya kare matakin da ya dauka tare da bayyana cewa yanci da niyyar demokaradiya na 'yan kasar Kenya ba za su zama ba wasu abun fadi ga kotunan waje ba. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China