Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai. Ya ce, warware batun nukiliyar kasar ta Iran nan ba da dadewa ba, za ta yi tasiri sosai kan hana yaduwar makaman kare dangi da kuma halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya.
Ya ce, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da dukkan bangarorin da abin ya shafa wajen mayar da hankali kan manyan matsaloli ta yadda kowane bangare zai samu abin da yake bukata a yarjejeniyar sannu a hankali.
Kasar Iran da kasashen da batun shirin nulikiyar kasar ya shafa da suka hada da Sin, Faransa, Burtaniya, Amurka da Jamus, za su ci gaba da sassantawa don ganin an cimma yarjejeniyar warware wannan batu.
Wang Qun, babban darektan sashen hana yaduwar makamai na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ne zai jagoranci tawagar Sin a tattaunawar da za a yi ranar 18 ga watan Janairu a birnin Geneva. (Ibrahim)