in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran ta ce akwai wuya a cimma yarjejeniyar nukiliya a ranar da aka tsai da
2014-11-24 10:15:19 cri

Akwai wuya a kai ga cimma wata hadaddiyar yarjejeniyar nukiliya kan nan da ranar da aka tsai da, cewa da ranar 24 ga watan Nuwamba, in ji wani jami'in tawagar kasar Iran da kamfanin dillancin labarai na daliban kasar Iran ya rawaito. A cewar wannan jami'in da aka sakaya sunansa, akwai wuya sosai a kai ga cimma wata yarjejeniya kafin ranar Litinin dalilin cewa, akwai wasu batutuwan da ya kamata a tattauna. Shawarar gusa yarjejeniyar ta Geneva za ta kasance kan tebur, idan ba za mu iyar cimma wata yarjejeniyar siyasa ba kafin ranar Lahadi da dare bisa agogon Vienna, in ji jami'in Iran.

Iran da manyan kasashe shida wato Burtaniya, Sin, Faransa, Rasha, Amurka da Jamus za su yin kokarin kai ga cimma wata yarjejeniyar siyasa da za ta kunshe da manyan batutuwa maimakon hadaddiyar yarjejeniya.

Sakataren harkokin wajen kasar Amurka, John Kerry ya bayyana damuwa iri guda. Muna fatan cewa, muna samun ci gaba sannu a hankali, amma har yanzu akwai manyan batutuwan da ba'a warware ba, in ji mista Kerry a ranar Asabar a cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa tare da ministan harkokin wajen kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier. Iran da manyan kasashe shida na gudanar da shawarwari a birnin Vienna domin cimma wata yarjejeniya da za ta tabbatar da cewa, shirin nukiliyan Iran yana amfanin jama'a ne.

Mista Kerry ya bayyana cewa, yarjejeniyar za ta rage karfin nukiliyan Iran sosai domin ganin cewa, wannan kasa ba za ta samu damar sarrafa shi ba domin kera makaman nukuliya a cikin shekara guda. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China