Li Keqiang ya bayyana cewa, babban taken ranar biranen kasa da kasa shi ne "birane dake taimakawa samun ingancin zaman rayuwa", kuma taken shekarar bana shi ne "canje-canje da kuma ci gaban birane", wanda ya nuna yanayi da kuma amfanin birane sosai, ya kuma nuna tunanin jama'a kan ci gaban birane a a cikin wannan zamani.
Mista Li ya kara da cewa, kasar Sin ita ce babbar kasa mai tasowa kuma mai yawan al'umma sama da biliyan 1.3, kana dukkanin nasarorin da kasar ta samu su ne domin yadda kasar ta yi kwaskwarima a gida. A cewar firaministan kasar za ta ci gaba da bin hanyar raya birane don samun ci gaban kasar.
A nasa sakon, babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya ce, an sanya ranar biranen kasa da kasa sakamakon taron baje kolin duniya da aka yi a birnin Shanghai na kasar Sin a shekarar 2010, kana taken ranar ya jaddada muhimmancin kawo kwaskwarima a birane, saboda kokarin kafa wasu biranen dake da muhalli masu inganci yana da muhimmiyar ma'ana ga jama'a, kana aikin na da muhimmanci wajen samar da hanyoyin neman dauwamammen ci gaban kasar. (Maryam)