Jiya Litinin gwamnatin kasar Amurka ta ce, karin takunkumi a kan kasar Iran ba zai yi tasiri ba musamman saboda manyan kasashen duniya sun rigaya sun amince da tsawaita tattaunawarsu da Iran, a kan makamashin nukiliya nan da watanni 7 masu zuwa.
Kakakin fadar ta White House Josh Earnest, a yayin da yake mai da martini a kan kiran da wadansu 'yan majalisar dokokin Amurka suka yi na neman a karawa Iran takunkumi, bayan da tattaunawar da aka yi da kasar ta ci tura a Vienna na Austria, ya ce, karin takunkumi a kan Iran a daidai lokacin da ake ci agaba da tattaunawa da kasar ba zai yi wani tasiri ba.
Duk da yake cewar sakataren harokokin wajen Amurka John Kerry ya ce, an samun gaggarumin ci gaba a tattaunawarsu da Iran, to amma sun kasa samun daidaito a kan manyan abubuwa guda biyu.
Bangarorin biyu dai sun kasa samun daidaito a kan ko injunan makamashin nukiliya nawa ya kamata Iran ta yi amfani da su a karkashin yarjejeniyar tasu da kuma tsawon lokacin da za'a dauka kafin a dage takunkumin da aka kakabawa kasar ta Iran.
A halin da ake ciki dai Iran da kasashen Amurka, Rasha, Britania, Sin, Faransa da Jamus sun yanke shawarar za su ci gaba da tattaunawa da juna har zuwa ranar 1 ga watan Yuli na shekarar badi. (Suwaiba)