Kakakin majalisar dokokin kasar Iran ya ce, Iran ba za ta amince ba da bukatun manyan kasashen duniya na hana mata walwala a shirinta na makamashin nukiliya, ba wanda ta ce na amfani cikin gidanata ne, to amma ya ce, Iran din, a shirye take ta goyi bayan matakan tattaunawa masu ma'ana game da shirin na nukiliya.
Kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya ce, kakakin majalisar dokokin kasar wanda yake jawabi a wani zaman taro na majalisar, Ali Larijani ya bukaci sauran bangarorin dake cikin tattaunawar ta makamashin nukiliyar na Iran da su kaucewa abin da ya kira hali na yaudara a yayin da ake gudanar da tattaunawa.
Tun farko a ranar Asabar da ta wuce, wani babban jami'i dake jagorantar 'yan kasar Iran a tattaunawar da ake yi, Abbas Araqchi, ya ce, kasar ta Iran ba za ta ja da baya ba game da 'yancin da take da shi na mallakar makamashin nukiliyar, duk kuwa da yake cewar, akwai barazanar fuskantar kalubale.
A watan Yulin da ya shude ne Iran da kasashen P5 wadanda suka hada da Britania, kasar Sin, Faransa, Rasha da Amurka kuma Jamus suka amince da karin wa'adin tattaunawar, har watanni hudu, watau zuwa nan da 24 ga watan Nawumba mai zuwa.
To amma bangarorin biyu sun gana a makon jiya a Vienna na Austria, sai dai har yanzu, babu wani haske a game daidaiton tattaunawar da aka yi. (Suwaiba)