in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a ci gaba da daukar matakan warware matsalar nukiliyar Iran, in ji Kerry
2014-07-16 10:19:33 cri

Sakataren wajen kasar Amurka John Kerry, ya ce, za a ci gaba da daukar matakan da suka wajaba, domin cimma nasarar da ta dace game da batun nukiliyar kasar Iran, a daidai gabar da ake ci gaba da cimma nasarori game da hakan.

Kerry wanda ya bayyana hakan a jiya Talata, ya ce, ya zuwa yanzu akwai sauran muhimman batutuwa da ba a kai ga warware su ba game da wannan batu, ko da yake dai bai yi wani karin haske game da hakan ba.

Kalaman na Kerry dai na zuwa ne, bayan doguwar tattaunawa da bangarorin masu ruwa da tsaki suka yi da wakilan kasar Iran, gabanin cikar wa'adin cimma matsaya kan yarjejeniyar karshe game da nukiliyar kasar.

A wani ci gaban kuma, mahukunta a Iran sun bayyana fatan cimma matsaya guda, game da batun nukiliyar kasar nan da ran 20 ga watan nan na Yuli, dake a matsayin wa'adin karshe da aka gindaya.

A cewar mai shiga tsakani na kasar Iran game da batun na nukiliya Mohammad Javad Zarif, kasarsa na fatan warware dukkanin batutuwan da ke da alaka da wannan batu, a daidai gabar da suke kara kwazo wajen sauke nauyin dake kan su a wannan fanni. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China