Wang Yi yaYa lura cewar tattaunawar da ake yi game da batun nukiliyar kasar Iran din ya samu cigaba sosai a lokutan bayan nan. Yace Sin a matsayin ta n a kasar da take cikin batun sassantawa cikin mutunci a kullum tana mai d a hankali ne akan tattauna da neman hanyar cimma daidaito cikin lumana wanda zai tafi dai dai da dokokin moriyar kasa da kasa har d a ita kanta Iran din.
A nashi bangaren Javad Zarif, ya yaba matuka game da gudunmuwa mai ma'ana da shawarwari mai hangen nesa da kasar Sin take bayarwa game da batun nukiliayar kasar sa.
Yace Iran a shirye take ta cimma amincewar da ake fata kuma tana da burin ganin ta cigaba da hulda da kasar Sin a kan lamarin don inganta tattaunawar yadda ya kamata.
Masu shiga ruwa da tsaki akan batun nukiliyar na kasashen P5+1 wato kasashen 5 na dindindin din a MDD da kuma ita kanta Iran din sun hallara Vienne babban birnin kasar Australiya domin tattaunawa na musamman dangane da cikan wa'adin batun a yau din nan 24 ga watan Nuwamba.
Dukkan bangarorin basu cimma matsaya akan sauran manyan batutuwa da suka rage ba kamar yadda kasashen yammacin ke son Iran ta bar batun nukiliyar baki daya ita kuma tace tana da 'yancin yin amfanin da nukiliayar ta babu tantama.