Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Qin Gang ne ya bayyana hakan yau yayin taron manema labarai a nan birnin Beijing.
Kasar Sin ta bukaci sassan da abin ya shafa, da su yi kokarin cimma wata yarjejeniyar da za ta kawo karshen wannan batu cikin ruwan sanyi.
Qing Gang ya ce, babban darektan sashen hana yaduwar makamai na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Qun ne zai jagoranci tawagar kasar Sin a wannan tattaunawa.
Kasar Iran da manyan kasashen duniya sun amince su kara wa'adin tattanauwar ce zuwa ranar 30 ga watan Yunin shekara ta 2015, don kara samun lokaci da damar cimma madafa.
Idan ba a manta ba a ranar 24 ga watan Nuwamba ne bangaren Iran da manyan kasashen duniya 6 da wannan batu ya shafa suka cimma wata yarjejeniya bayan an gaza cimma kwakkwarar matsaya. A karkashin kwarya-kwaryar yarjejeniyar, Iran ta amince ta dakatar da wasu ayyukanta na nukiliya domin a sassauta mata takunkumin da aka kakaba mata. (Ibrahim)