Wasu manyan kusoshin gwamnatin Amurka da na kasar Iran sun fara gudanar da wani taro na kwanaki uku a kan makamashin nukiliya na kasar Iran mai cike da takaddama jiya Alhamis a Geneva.
Shi wannan taro kamar wani share fage ne a game da tattaunawar da za'a yi a ranar 18 ga wannan wata, kuma ana sa ran tattaunawar za ta samu halarcin manyan kasashe na duniya da kuma Iran din kanta.
Wata tawagar Amurka dake Geneva ta bayar da tabbaci cewar, tawagar muhawarar kasar Amurka tana karkashin jagorancin mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka Wendy R. Sherman, da kuma tsohon mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka William Burns, da kuma manyan mashawarta kamar su Jake Sullivan da Rob Malley.
Ita kuma tawagar Iraqi tana karkashin jagorancin mataimakin ministan harkokin wajen kasar Abbas Araqchi da kuma Majid Takht Ravanchi. Akwai kuma kwararru daga bangarorin biyu masu taka rawa a taron.
An samu nasarar shirya wannan taron ne bayan da sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya gana a karo da dama da ministan harkokin waje na kasar Iran Mohammed Javad Zarif, inda suka tattauna a kan batutuwa da dama. (Suwaiba)