in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Amurka da Faransa na ci gaba da matsa lamba game da batutuwan Iran da Siriya
2014-02-12 15:22:22 cri
Shugaba Barack Obama na Amurka, da takwaransa na kasar Faransa Francois Hollande, sun amince da ci gaba da yin matsin lamba game da batutuwan da suka shafi kasashen Iran da Siriya.

Shugabannin biyu sun cimma wannan matsaya ne yayin ganawar su a fadar White House dake Amurka a ranar Talata 11 ga wata.

Yayin taron manema labaru da aka shirya cikin hadin gwiwa bayan shawarwarin, Obama da Hollande sun amince da ci gaba da kakabawa Iran takunkumi, kamar yadda ya ke a yanzu.

Cikin mako mai zuwa ne dai kasar Iran, da kasashe 6 da batun nukiliyar ta ya shafa, za su yi shawarwari a birnin Vienna da ke kasar Austria, matakin da ake fatan zai kawo dama ga kasar ta Iran, ta lalubo bakin zaren warware batutuwan da suka shafe ta.

Game da masana'antun kasar Faransa da yawa dake Iran suna gudanar da hada hadar kasuwanci, sakamakon sassaucin da a baya kasashen Amurka da na Turai suka yiwa kasar ta fuskar takunkumi, Obama ya yi kashedin cewa, matakin da aka dauka yanzu zai haifar da sabon kalubale.

Shi kuwa a nasa bangare shugaba Hollande cewa ya yi, ba zai hana shugabannin kamfanonin kasar sa gudanar da kasuwanci ba, amma ya tabbatar musu cewa, za a ci gaba da aiwatar da takunkumin da aka saka wa Iran, kafin Iran din ta daddale yarjejeniya tare da kasashe 6 da batun nukiliyar ta ya shafa, ba kuma za su daddale wata yarjejeniyar kasuwanci tare da Iran din ba kafin wannan mataki.

Game da batun Siriya, Obama ya ce, barazanar daukar matakan soji a kan ta, ya haifar da shirin kawar da makamai masu guba a kasar Siriya, don haka ya ce kamata ya yi Siriya ta cika alkawarin da ta dauka, kuma Rasha tana da hakkin tabbatar da hakan.

Yayin da bangarorin Siriya biyu ke daf da ci gaba da shawarwari a birnin Geneva, kasashen Amurka da Faransa za su ci gaba da goyon bayan bangaren masu sassaucin ra'ayi cikin bangarorin 'yan adawar kasar, a sa'i daya kuma, sun yi kira ga kasashen duniya da su hana dakaru masu dauke da makamai na kasashen waje shiga kasar ta Siriya. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China