Shugaba Hollande ya bayyana hakan ne bayan ganawarsa da takwaransa na kasar Togo, Faure Essozimna Gnassingbé a fadar sa dake birnin Faris. Hollande ya bayyana wa kafofin yada labaru cewa, gwamnatin Faransa na kokarin yin binciken sakwannin da aka samu, dongane da wannan malamin addini, zai kuma yi shawarwari da takwaransa na Kamaru kan wannan batu.
Dadin dadawa, shugaba Hollande ya furta cewa, kawo yanzu Faransa tana maida hankali sosai kan batun yaki da ta'addanci. Yace koda yake aikin soja da Faransa ta yi a kasar Mali a bana ya yi babbar nasara, tare da taimakawa gwamnatin Malin wajen maido da cikakken yankin tsaro, duk da haka gwagwarmayar da Faransan ke yi da ta'addanci ba ta kare ba.
Yace ta'addanci na fitowa ta hanyoyi daban daban, kuma ba kasafai ya kan fito ta hanyar da ake tsammani, ko wuri mafi hadari ba.(fatima)