Mr.Le Drian ya kara da cewa, jirgin saman ya tashi ne daga wani sansanin sojojin sama dake yankin babban birnin kasar Nijer,kuma babu sojojin kasa da suka shiga kai harin. Kasar Amurka a nata bangaren, ta samar da taimakon fasahohi na binciken maboyar 'yan tawayen da dai sauransu.
Kakakin babbar hedkwatar ba da umarni ga rundunar soja ta kasar Faransa, kanar Gilles Jaron a sanarwar da ya fitar ya ce, jirgin saman soja maras matuki ya gano wani sansanin sirrin kungiyar Al-Qaida dake yankin Adrar, yayin da ke gudanar da aikinsa na yin bincike, sa'an nan, jirgin sama ya kai farmaki ga dakarun. A halin yanzu, sojojin kasar Faransa na aiwatar da manyan ayyukan soja a wannan yanki. (Maryam)