Sanarwar ta kuma nuna cewa, an yi garkuwa da wannan malami ne a ranar Laraba 13 ga wata da dare a wani yankin arewacin kasar Kamaru dake da nisan kilomita 30 da iyakar kasashen Kamaru da Nijeriya. A halin yanzu, gwamnatin kasar Faransa tana tattaunawa da gwamnatin kasar Kamaru don sanin halin da ake ciki ta yadda za a ceto malamin cikin sauri.
Amma zuwa yanzu, babu wanda ya sanar da daukar alhakin sace malamin.
Yanzu kasar Faransa ta riga ta ayyana yankin arewacin kasar Kamaru a matsayin yanki mai hadari inda ta shawarci 'yan kasarta da kada su je yankin. (Maryam)