in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Faransa da Iraki suna fatan za a gudanar da taron kasa da kasa kan batun tsaron kasar Iraki cikin hanzari
2014-09-03 10:37:04 cri
Kafofin watsa labaru na kasar Faransa sun ruwaito fadar shugaban kasar na cewa, shugaban kasar Francois Hollande ya zanta ta wayar tarho tare da shugaban kasar Iraki Muhammad Fuad Masum, inda suka yi musayar ra'ayoyi kan kiran da Hollande ya yi a watan Agusta na bana game da gudanar da wani taron kasa da kasa kan batun tsaron kasar Iraki, inda shugabannin biyu ke fatan za a hanzata yin taron.

Fadar shugaban kasar Faransa ta yi nuni da cewa, Masum yana ganin cewa, kiran wannan taron kasa da kasa kan batun tsaron kasar Iraki yana da muhimmanci. Shugabannin biyu sun kuma tattauna kan hanyar sa kaimi ga gudanar da taron cikin sauri, tare da tsaida kudurin sake tattauna batun cikin kwanaki masu zuwa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China