in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala taron Elysee kan zaman lafiya da tsaro a Afrika
2013-12-08 16:16:52 cri
An kammala babban taron Elysee kan zaman lafiya da tsaro a nahiyar Afrika a ranar Asabar a birnin Paris na kasar Faransa inda a karshen taron aka fitar da wata sanarwar karshe da ta samu amincewar illahirin wakilan kasashen Afrika 53 da suka halarci wannan zaman taro, har da shugabannin kasashe kusan arba'in da gwamnatoci.

Sanarwar da fadar shugaban kasar Faransa ta gabatar a karshen taron na kwanaki biyu ta maida hankali kan muhimman batutuwa uku da kasar Faransa da kasashen Afrika suka tattauna kansu da suka hada da tabbatar da zaman lafiya da tsaro, cigaban tattalin arziki da kuma rigakafin sauye sauyen yanayi.

Game da batun tsaro, sanarwar ta nuna cewa mahalarta taron sun yi kira da a karfafa tattaunawa mai nagarta tsakanin Afrika da Faransa bisa tushen tsinkaye na hadin gwiwa domin fuskantar barazana, tare da maida hankali bisa muhimmancin tsarin dangantaka da zai iya amsa bukatun duniya na wannan lokaci, bisa tushen MDD dake da karfi da wani sabon salo.

Haka kuma sanarwar ta jaddada musamman ma niyyar kasar Faransa na taimakawa kokarin kungiyar tarayyar Afrika AU na cika nauyin dake bisa wuyanta ta kafa wata rundunar sojojin Afrika nan da shekarar 2015, haka ma da karfin wannan runduna da ta Afrika wajen amsa bukatun gaggawa na warware matsaloli kamar yadda kungiyar AU ta dauki niyya a watan Mayun shekarar 2013.

Tawagogin kasashen Afrika 53 da suka harlarci wannan taron sun hada da shugabannin Afrika da dama da ma shugabannin gwamnatocin nahiyar, musammun ma shugaban kasashen Mali Ibrahim Boubacar Keita, shugaba Mahamadou Issoufou na kasar Nijar, shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara da shugaban kasar Najeriya mista Goodluck Jonathan. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China