Shugaban kasar Sin Xi jinping ya bugawa takwaransa na kasar Faransa François Hollande wayar tarho a ranar alhamis din nan 8 ga wata domin bayyana takaici da bakin ciki kan harin da aka kai a birnin Paris, tare kuma da yin tir da harin da aka kai da nuna juyayi ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu, da kuma wadanda suka ji rauni.
A lokacin da suke zantawa ta wayar, shugaba Xi ya ce, ta'addanci babban makiyi ne ga al'ummar duniya, kuma barazana ce ga Sin da Faransa har ma dukkanin kasashen duniya gaba daya. Don haka Sin na yaki da duk wani aikin ta'addanci, kuma tana fatan hada kai da Faransa don karfafa karfinsu na tabbatar da tsaron kasashensu da yaki da ta'addanci, sannan kuma da kiyaye zaman lafiyar kasashen biyu da daukacin duniya, har ma da kiyaye lafiyar jama'ar kasa da kasa. (Amina)