Bisa kididdigar da hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta bayar a ran 29 ga wata, an nuna cewa, ya zuwa ran 27 ga wata yawan mutanen da suka kamu da cutar Ebola a kasashen uku na yammacin Afrika wato Saliyo, Laberiya, Guinea ya kai 20081, daga cikinsu mutane 7842 sun mutu.
A halin yanzu, kasar Saliyo ta zarce Laberiya da yawan mutanen da suka kamu da cutar Ebola, wadanda yawansu ya kai 9409, daga cikinsu 2732 sun mutu. A dalilin haka ne ma, kasar ta Saliyo ta soke duk wasu bukukuwan bikin Kirismas da na shiga sabuwar shekara domin hana yaduwar wannan cuta. (Amina)