Shugaban kasar Ghana John Drahami mahama ya gana da magatakardar MDD Ban Ki-moon wanda ya isa kasar a ranar Alhamis din nan, inda suka tattauna matakan da duniya da kuma shiyya shiyya suka dauka game da cutar Ebola a yankin yammacin Afrika.
Kamar yadda wata sanarwa daga fadan shugaban kasar ta Ghana ta yi bayani, ganawar ta zo ne gabannin ziyarar da magatakardan MDD zai kai kasashe uku da cutar ta fi kamari a yammacin Afrika wato Guinea, Saliyo da kuma Liberiya a Jumma'an nan.
Kasar Ghana dai ta janyo hankulan kasashen duniya matuka a game da cutar ta Ebola a yankin yammacin Afrika, sakamakon ziyarar shugaba Mahani wanda kuma shi ne shugaban kungiyar tattaliun arzikin kasashen yammacin Afrika wato ECOWAS zuwa kasashe uku da cutar ta fi kamari.
An dai kafa hukumar matakin gaggawa a kan cutar ta Ebola UNMEER ne a babban birnin kasar ta Ghana wato Accra. (Fatimah)