Kwamitin tattalin arzikin MDD reshen Afrika (CEA) ya fitar da wani rahoto a ranar Litinin a birnin Addis Abeba kan tasirin da cutar Ebola ga al'umma da tattalin arziki a kasashen Guinea, Saliyo da Liberiya.
Ya kamata, kungiyoyin ba da lamuni da kasashen dake biyar bashi su yi tunani sosai domin soke bashin waje na wadannan kasashe uku, in ji wannan rahoto. Tashin hankali da rudani da wannan cuta ta hadasa, da kuma tasirin Ebola ga mace macen mutane, sun janyo faduwar ayyukan tattalin arzikin a wadannan kasashe uku, a cewar rahoton. Wannan matsala ta ci bashi na nuna wasu abubuwan koma baya, da suka hada faduwar ciniki a kasuwanni da manyan shaguna, raguwar ayyukan dakunan cin abinci, otel, ayyukan gine gine, sufuri da ilimi, haka ma da matakan da gwamnati ta dauka kamar kafa dokar ta baci da takaita zirga zirgar jama'a, in ji wannan rahoto. Faduwar kudin shiga da gwamnati ke samu za ta iyar cimma dalar Amurka miliyoyi gomai, abin dake wakitar wani adadin da ba na wasa ba na GDP a wadannan kasashe uku, a cewar rahoto. (Maman Ada)