An ce, wannan ne karon farko da kasar Sin, da hukumar shirin samar da abinci ta duniya WFP, suka yi hadin gwiwa wajen yaki da cutar Ebola a kasar Guinea. Karkashin hukumar ta WFP, za a yi jigilar gudummawa kayan da suka hada da shinkafa, da biskit da sauransu, wadanda darajarsu ta kai dala miliyan 2.
Wakiliyar hukumar WFP dake kasar Guinea Elisabeth Faure, ta bayyana a gun bikin mika gudummawar cewa, tun daga watan Afrilun bana, hukumar ta WFP ta riga ta samar da abinci har ton kimamin dubu 10, ga yankuna mafiya fama da cutar Ebola a kasar ta Guinea. A ganinta, aikin ba da gudummawa da kasar Sin ta yi a wannan karo, alama ce ta zumunci mai karko dake tsakanin Sin da Guinea, kana hakikanin mataki ne na hadin gwiwa tsakanin Sin da hukumomin kasa da kasa kamar hukumar ta WFP. (Zainab)