in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kira taron tattauna tsarin da za bi wajen horar da masana a fannin harsunan kasashen Afrika a nan birnin Beijing
2014-12-26 20:48:04 cri

An kira taron tattauna tsarin da za bi wajen horar da masana a fannin harsunan kasashen Afrika a ranar jumma'ar nan 26 ga wata a jami'ar Peking dake nan birnin Beijing. Masana daga jami'o'i daban-daban na kasar Sin kimanin 50 suka halarci taron, tare da yin musanyar ra'ayi kan yadda za a koyar da ilmin harsunan Afrika da tsarin da za a bi wajen horar da masana a wannan fanni.

Shugabar cibiyar nazarin adabin kasashen gabas na jami'ar Peking wadda ta jagoranci shirya taron Ferfesa Wei Liming ta ce, dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka na samun ci gaba cikin saurin a wadannan shekaru da suka wuce. A sa'i daya kuma, adabin harsunan kasashen Afrika yana ta kara janyo hankalin al'umma yayin da ake samun ci gaba sosai kan nazarin adabin duniya. Amma, ba da dadewa ba kasar Sin ta fara nazarin adabin harsunan kasashen Afrika, yadda za a daga matsayin manhaja da horar da masana a wannan fanni da sa kaimi fahimtar fasaha da adabin harsunan kasashen Afrika zai zama wani muhimmin aiki da masana a wannan fanni suke nazari. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China