An bude taron koli na uku tsakanin kasashen Larabawa da Afrika a jiya Talata 19 ga wata a birnin Kuwait na kasar Kuwait inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika da sakon fatan alheri ga taron da kuma mahalarta taron.
A cikin sakon sa da wakilin musamman na shugaba Xi Jinping kuma ministan harkokin cikin gidaLi Liguo ya karanta,Shugaba Xi ya darajanta ci gaba da kasashen Larabawa da Afrika suka samu wajen yin hadin kai a fannoni daban-daban, kuma ya yi imani da cewa, kasashen Larabawa da Afrika za su yi amfani da zarafi mai kyau wajen habaka hadin kai tsakaninsu.
Mr Xi ya ce Sin tana mai da muhimmanci sosai kan bunkasa dangantakar dake tsakaninta da kasashen Larabawa da kasashen Afrika, kuma tana fatan yin hadin kai da wadannan kasashe ta yadda za su ingiza dangantakar dake tsakanin su bisa manyan tsare-tsare.
A nashi bangaren Shugaban kasar Kuwait Sheik Sabah Al-Ahmad Al-Jaber Al-Sabah ya nuna godiya ga Shugaba Xi bisa ga fatan alherinsa sosai. (Amina)