A jawabin da ya gabatar Duan Shijie ya yi bayani kan matsayin da gwamnatin Sin ke kai wajen yaki da magungunan kara kuzari, da kuma manufar da take bi ta hana shan magungunan kara kuzari, da bincike game da masu amfani da magungunan, da kuma tabbatar da hukunta masu ta'ammali da magungunan. Har ila yau Duan Shijie ya kara da cewa, sabuwar ka'idar yaki da magungunan kara kuzari da za a fitar a cikin wannan shekara, za ta ba da tabbaci game da ayyukan yaki da ta'ammali da wadannan magungunan, tare da dokar da aka tanada kan sarrafa magungunan, da zartas da hukunci ga masu ta'ammali da su, da kulawa da abinci na 'yan wasanni da sauransu.
Taron da ya kasance irin sa na 4, a wannan karo an gudanar da shi ne a tsakanin ranakun 12 zuwa 15 ga wata, a birnin Johannesburg da ke kasar Afrika ta Kudu, kana kuma wannan shi ne karo na farko da aka yi wannan taro a nahiyar Afrika.
Masu ruwa da tsaki a harkar wasannin motsa jiki, da wakilan hukumar UNESCO, da jami'an kasashen duniya, da na kungiyoyin yaki da magungunan kara kuzari sama da 1000 ne suka samu halarci taron na bana. (Bako)