A wannan rana Mista Liu ya jagoranci taron kwamitin, inda aka zartas da shirin ayyukan da za a yi a watan Nuwamba. Daga baya, a gun taron manema labaru da aka yi bayan taron, Liu Jieyi ya bayyana cewa, kwamitin zai sha aiki a watan Nuwamba, inda za a kira taruruka har 30 wadanda za su shafi manyan batutuwa fiye da 20, daga cikinsu, akwai manyan batutuwa dangane da Afrika da batun yankin Gabas ta Tsakiya za su zama muhimman batutuwa a watan Nuwamba.
Game da kokarin da kotun hukunta manyan laifufuka ta kasa da kasa take yi na gurfanar da shugaban kasar Kenya a gaban kotun, a nasa bangare, Liu Jieyi ya nuna cewa, kasashen Afrika mambobin kwamitin sun riga sun gabatarwa kwamitin daftarin shiri, wanda suka nemi kotun da ta jinkirta lokacin gurfanar da shugaban Kenya a gaban kotun, kwamitin zai tattauna da bangarori masu ruwa da tsaki kan lamarin. Mista Liu ya kara da cewa, 'yan kasar Kenya ne suka zabi shugabansu, ya kamata a mutunta zabinsu. Sin sahihiyar abokiyar kasashen Afrika ce, ta fahimci damuwar Kenya da kungiyar tarayyar Afrika wato AU, kuma tana goyon baya kwamitin da ya amsa bukatun Kenya da AU yadda ya kamata. (Amina)