A ranar alhamis 6 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika da sakon ta'aziyya ga takwaransa na kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma game da rasuwar tsohon shugaban kasar Nelson Mandela.
A cikin Sakon, Shugaba Xi ya ce a madadin gwamnatin kasar Sin da jama'arta da shi kansa, yana nuna matukar juyayi game da rasuwar Mandela, kuma yana mika ta'aziyya ga gwamnatin kasar da jama'arta da kuma iyalan Mandela. Mr. Xi ya bayyana Mandela a matsayin wani mutumin da ba da babban taimako wajen raya dangantaka tsakanin kasashen Sin da Afrika ta Kudu, wanda a tsawon rayuwarsa ya ziyarci kasar Sin har sau 2, tare da yin hobbasa wajen inganta hadin gwiwa daga dukkan fannoni a tsakanin kasashen biyu.
A don haka jama'ar kasar Sin za su tuna da babbar gudummawa da Mandela ya bayar wajen raya alakar dake tsakanin kasashen biyu da ci gaban dan Adam baki daya. Xi Jinping ya jaddada cewa, yana fatan ci gaba da kokari tare da Mr. Zuma, don inganta dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare dake tsakanin kasar Sin da ta Afrika ta Kudu.(Bako)