Shen Danyang ya bayyana hakan a gun taron manema labaru da ma'aikatar harkokin ciniki ta kasar Sin ta gudanar a wannan rana. Tun daga farkon shekarar bana, an samu barkewar cutar Ebola a wasu kasashen yammacin Afirka bi da bi. Daga bisani gwamnatin kasar Sin ta samar musu da tallafi har sau hudu da yawansu ya kai kudin Sin Yuan miliyan 750. Amma wasu kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya sun bayar da labarin cewa, gudummawar da kasar Sin ta bayar ba ta taka kara ta karya ba.
Game da zancen, Shen Danyang ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta samar da gudummawa mafi amfani, kuma ta cika alkawarinta, don haka gwamnatocin kasashen da jama'ar da suka karbi gudummawar har ma da gamayyar kasa da kasa sun nuna yabo ga kasar Sin sosai.
Ban da wannan kuma, Shen Danyang ya yi nuni da cewa, kasar Sin tana daya daga cikin kasashen da suka fi samar da kudin taimako ga kasashe masu fama da cutar Ebola. Ana yin amfani da wadannan kudi a fannonin samar da kayayyakin rigakafi da yaki da cutar, samar da kudi da abinci, tura rukunonin masanan kiwon lafiya da likitoci, taimakawa wajen gina gidan gwaji da cibiyar bada jinya ga masu kamu da cutar a kasashe masu fama da cutar da dai sauransu. (Zainab)