in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojan Sin za ta ci gaba da taimakawa kasashen yammacin Afirka wajen shawo kan cutar Ebola
2014-11-27 20:37:29 cri

A yau Alhamis 27 ga wata, kakakin ma'aikatar tsaron kasar Sin Geng Yansheng ya bayyana cewa, rundunar sojan kasar za ta ci gaba da goyon baya da taimakawa kasashen yammacin Afirka wajen shawo kan cutar Ebola.

A gun taron manema labaru da aka shirya a wannan rana, mista Geng ya bayyana cewa, tun bayan yaduwar cutar Ebola a yammacin nahiyar Afirka, rundunar sojan kasar Sin ta tura daruruwan likitoci da masanan shawo kan cuttuttuka dake iya yaduwa da dai sauran ma'aikatan da aikin ya shafa masu ba da jagoranci da ba da tabbaci sama da dari daya sau da dama zuwa Saliyo da Liberiya domin gudanar da aikin ceto. Yanzu rukunin likitoci da aka tura karo na biyu zuwa Saliyo ya riga ya isa kasar, wanda yake share fagen canza cibiyar bincike zuwa cibiyar ba da jiyya, ta yaddakuma za a kara kyautata kwarewar ingancin likitoci da ingancin kayayyaki. Ban da haka, an riga an fara amfani da cibiyar ba da jiyya ga cutar Ebola da rundunar sojan Sin ta ba da kyauta ga Liberiya a ranar 25 ga wata. Sannan kuma, rundunar ta dauki nauyin tattara da jigilar kayayyakin agajin jin kai da Sin ta bayar ga kasashen yammacin Afirka dake fama da cutar Ebola.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China