Wata kungiyar jami'an kiwon lafiya daga gundumar Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin za ta tafi kasar Guinea-Bissau domin horas da jami'an kiwon lafiyan dake kasar a kan kariya daga cutar Ebola, kamar yadda hukumar kiwon lafiyar gundumar ta sanar.
Kungiyoyin da suka kasu kashi uku za su tashi a ranar Alhamis din nan kuma za su yi kwanaki 32 suna ba da horo a Guinea-Bissau ga jami'an kiwon lafiya kimanin 500.
Ya zuwa watan Oktoban wannan shekarar, kasar Sin ta tura jami'an kiwon lafiya da kuma likitoci 450 zuwa yammacin Afrika, ta kuma gina dakunan gwajin cututtuka da dakunan ba da jinya a yankin. (Fatimah)