Kasar Sin ta yi imani da cewa, sakamakon kokarin da kasashen Sin da Liberia suke yi cikin hadin gwiwa, tabbas Liberia za ta samu nasarar yaki da cutar Ebola, kamar yadda Hong Lei, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a yau Litinin 17 ga wata.
Mista Hong ya fadi haka ne a gun taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing, yayin da yake bayyana isar ma'aikatan lafiya na kasar Sin daga rundunar sojan kasar zuwa Liberia. Hong ya kara da cewa, wadannan ma'aikatan lafiya 163 da suka fito daga rundunar sojan kasar Sin sun isa Monrovia, babban birnin Liberia a ranar 15 ga wata, inda za su fara aiki a cibiyar kula da masu fama da cutar Ebola jinya, wadda kasar Sin ta taimakawa wajen gina ta kuma za ta fara karbar masu fama da cutar a ranar 25 ga wata. Wadannan ma'aikatan lafiya za su yi kokarin kubutad da masu fama da cutar Ebola tare da horas da takwarorinsu na Liberia tare da koyar musu fasahohin kasar Sin na yin rigakafin cututtuka masu yaduwa.
Mista Hong ya ci gaba da cewa, kasar Sin ce ta gina cibiyar, inda ma'aikatan lafiyan Sin za su yi aiki a ciki, kuma bangaren Sin zai tafiyar da ita, lamarin da ya zuwa yanzu bai taba ganin irinsa a dukkan ayyukan da kasashen duniya suka yi domin taimakawa kasashen yammacin Afirka wajen yaki da cutar ba. (Tasallah)