Kayayyakin da aka samar wa jihar a wannan karo sun hada da abin rufe baki, safar hannu, tufafi, abinci da dai sauransu. Daga cikin wadanda suka halarci bukin samar da kayayyakin akwai, Shugaban reshen kungiyar, mai kula da harkokin daidaitawa na kungiyar musamman mai kula da harkokin gaggawa wajen yaki da cutar Ebola ta MDD dake kasar Liberia, da gwamnan jihar Sinoe, da shugaban ofishin 'yan sanda na jihar da wasu jami'an hukumomin kasa da kasa da na jihar Sinoe.
Tun dai a karshen watan Yuni ne, cutar Ebola ke ci gaba da yaduwa a kasar Liberia, wannan ya sa a kwanan baya, 'yan sandan kiyaye zaman lafiyar kasar Sin dake kasar Liberia sun ba da gudunmawar kudi ga kasar, kuma sun yi amfani da kudaden da suka bayar wajen sayen kayayyakin da suka gabatar a ran 25 ga watan da muke ciki. (Maryam)