in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagogin Sin guda 4 sun tafi aikin dakile Ebola a yammacin Afrika
2014-11-15 10:18:26 cri

Wasu tawagogi guda hudu masu kunshe da ma'aikatan kiwon lafiya, jami'an kiwon lafiya su kimanin 205 a daren Jumma'an nan suka tashi zuwa kasashen yammacin Afrika domin taimaka musu dakile cutar Ebola.

A lokacin aikin nasu, za su samar da aikin jinya da kuma matakan kariya ga al'umma a kasashe uku da wannan annoba ta fi shafa wato kasashen Liberiya, Saliyo da kuma Guinea.

Ya zuwa yanzu, kasar Sin ta aika fiye da jami'an kiwon lafiya 300 zuwa yammacin Afrika, sannan da kusan ma'aikata da jami'an kiwon lafiya 1,000 suna zaune cikin shirin ko ta kwana.

Gwamnatin kasar Sin ta kuma samar da taimakon kudi da kayayyakin aiki ga wadannan kasashe da ya kai kimanin yuan miliyan 750, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 122.

Gina dakin duba tare da ba da jinya ga masu dauke da cutar a Liberia da taimakon gwamnatin kasar Sin, ana sa ran kammala shi a ranar 25 ga watan nan da muke ciki, a cewar Mao Qun'an, kakakin kwamitin kiwon lafiya da kayyade haihuwa na kasar.

Mao ya ce, taimakon magunguna daga kasar Sin ga wadannan kasashe shi ne mafi girma da wata kasa ta yi, kuma zai taimaka matuka tare da ciyar da huldar abota tsakanin Sin da kasashen Afrika. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China