in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta samar da kudin kyauta dalar Amurka miliyan 6 ga asusun tinkarar cutar Ebola na M.D.D.
2014-12-02 21:23:23 cri

A ranar Talata 2 ga wata, Mr Zhang Xiangchen, mai ba da taimako ga ministan kasuwancin kasar Sin, wakilin gwamnatin kasar Sin da Alain Noudehou, babban wakili mai kula da aikin daidaita harkokin ofisoshin M.D.D. da na hukumar raya kasashe ta UNDP dake nan kasar Sin sun sa hannu kan takardar kyautar kudin da kasar Sin ta samar na dalar Amurka miliyan 6 ga asusun tinkarar cutar Ebola na M.D.D. a nan kasar Sin.

A jawabinsa, Mr. Alain Noudehou ya nuna godiya ga taimakon da gwamnatin kasar Sin ta bayar na tinkarar cutar Ebola, ya kuma jaddada cewa, zai kara yin kokarin karfafa kyakkyawar dangantaka tsakanin M.D.D. da kasar Sin. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China