Sashen kula da tsare-tsare na sojojin 'yantar da al'umma ta kasar Sin wanda ya bayyana hakan a yau ya ce, cibiyar nazarin aikin likita ta sojojin kasar Sin ce ta samar da allurar ta yadda za ta dace da nau'in kwayoyin halittun bil-adama musamman wadanda ke yammacin Afirka.
A halin yanzu an hada allurar ce a matsayin garin foda, inda za ta iya zama na tsawon makonni biyu a yanayin da ya kai digirin 37 na ma'aunin celcius ba tare da lalace ba.
Wani nazari da wasu kwararru kimanin 17 suka yi ya nuna cewa, an yi amfani da wannan dabara ce ta yadda allurar za ta dace da yanayin zafi na yammacin Afirka. (Ibrahim Yaya)