in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yaba wa kasar Sin bisa taimakon da ta samar domin yaki da cutar Ebola
2014-12-16 20:37:34 cri
A jiya Litinin 15 ga wata ne, aka bude taron musamman na ministocin kiwon lafiya na kungiyar tarayyar kasashen kudu maso gabashin nahiyar Asiya ta ASEAN da kasashen Sin, Japan da kuma Koriya ta Kudu a birnin Bangkok na kasar Thailand, inda wakilai mahalarta taron suka tattauna kan yaki da cutar Ebola ta hanyar karfafa hadin gwiwar ayyukan kiwon lafiya a yankin, haka kuma, a yayin taron, mahalarta taron sun yaba wa kasar Sin bisa ga taimakon da ta baiwa kasashen yammacin Afirka, da suka hada da kayayyakin agaji da masanan kiwon lafiya da ta aike zuwa kasashen da cutar ta shafa cikin sauri.

Kimanin mutane 100 da suka hada da ministocin kasashe 10 na kungiyar ASEAN, ministocin kasashen Sin, Japan da kuma Koriya ta Kudu, babban sakataren ofishin sakatariyar kungiyar ASEAN da wasu jami'an hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ne suka halarci wannan taro.

Wakilan kasar Sin karkashin jagorancin mataimakiyar shugaban hukumar kula da harkokin kiwon lafiya da tsara iyali Cui Li sun halarci taron, a jawabin da ta gabatar ta bayyana irin ayyukan taimako da goyon bayan da kasar Sin ta samar wa kasashen yammacin Afirka dake fama da cutar Ebola da kuma wasu kasashen dake kewaye da wadannan kasashe, ta kuma ba da wasu shawarwari dangane da yadda za a iya karfafa hadin gwiwar kungiyar ASEAN da kasashen Sin, Japan da Koriya ta Kudu ta fuskar yin rigakafi da hana yaduwar cutar Ebola. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China